Malaysia za ta dawo da ‘yan kasarta daga yankunan arewa da yammacin Indiya yayin da yawan wadanda ke kamauwa da COVID-19 ke ci gaba da karuwa a kasar da ke Kudancin Asiya.
Ministan Harkokin Wajen Hishammuddin Hussein ya ce kasarsa za ta yi amfani da wani jirgin sama na musamman da aka yi haya don taimakawa dawowar ‘yan kasarta.
Hussein ya ce "Jirgin zai tashi zuwa New Delhi da Mumbai da zaran gwamnatin Indiya ta ba da amincewa kuma an kammala dukkan shirye-shirye,"
Ba a sanya yankunan kudu da gabashin Indiya a cikin yankunan da za'a kwaso yan kasar a halin yanzu.
Ya nemi Malesiyawan da ke zaune a yankunan arewaci da yammacin Indiya da su yi rajista da ofishin jakadancin Malesiya a Mumbai idan suna son komawa gida