Annobar Korona ta kara kamari a kasashen Latin Amurka

Annobar Korona ta kara kamari a kasashen Latin Amurka

Kasashen Latin Amurka sun bayyana karin yawan kamuwa da mace-mace daga kwayar cutar Korona a kasashensu.

Kasar Brazil ta ba da rahoton mutuwar mutane 1,099 da karin 40,054 da suka kamu da cutar a ranar da ta gabata.

Adadin wadanda suka mutu a kasar yanzu ya kai 560,706, yayin da adadin wadanda suka kamu ya haura miliyan 20.6.

Kamar yadda jaridar Daily Sabah ta rawaito, a Meziko, an sami mutuwar mutane 618 da karin kamuwa da Korona har mutum 21,569 a cikin awanni 24 da suka gabata.

Adadin wadanda suka mutu a Argentina ya karu da 276 a ranar da ta gabata, jimlar mutuwar mutanen ya kai 107,023.

Ma'aikatar Lafiyar Kolombiya ta ba da rahoton wadanda suka rasa rayukansu har su  204 a cikin ranar da ta gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga cutar a kasar ya kai 121,899.


News Source:   ()