Za a rufe wani gidan yari na wani dan lokaci saboda matsalar bera a jihar New South Wales dake kasar Australia.
Kamar yadda jaridun kasar suka rawaito, jami’in gidan yarin Wellington, Peter Severin ya sanar da cewa za a sauya fursunoni da ma’aikatan su 420 zuwa wani gidan yarin.
Da yake jaddada cewa lafiyar fursunoni da na ma'aikata shi ne abin da ya fi muhimmanci, Severin ya ce ya kamata a dauki wannan matakin domin a kauda berayen daga gidan yarin.
An tabbatar da cewa beraye na haifar da matsalar tsaro ta hanyar cinye wayoyin sadarwa da na wutar lantarki da kuma lalata rufin sili a gidan yarin.
A labaran an nanata cewa sanadiyar ibtila'in barayen da suka yawaito a yankin an yi hasarar kayayyakin da kudinsu ya kai gomman miliyoyin daloli a yankin.