
A cikin rahoton da ƙungiyar ta CPJ ta fitar a yau Laraba, ta ce an samu ƙarin kashi 22 na ƴanjaridar da aka kashe a shekarar 2023, lamarin da ya sa ta bayyana shekarar bara a matsayin mafi muni wajen kisan ƴanjarida a cikin shekaru 30 da suka gabata.
Ta ce a yaƙin Isra’ila da Hamas, ƴanjarida 85 hare-haren sojojin Isra’ila ya hallaka, kuma daga cikinsu 82 Falasɗinawa ne.
Haka nan ƙasashen Sudan da Pakistan ke zaune a mataki na biyu, inda rahoton ya ce a shekarar da ta gabata an kashe ƴanjarida 6 – 6 a cikinsu, sai Mexico da ta yi ƙaurin suna wajen kisan manema labarai da aka kashe 5 a cikinta.
Rahoton na CPJ ya kuma gano cewa a shekarar bara, an kashe ƴanjarida 2 a Haiti da ke fama da rikicin ƴandaba, sannan aka yi sauran kashe-kashen a ƙasashen Myanmar da Mozambique da India da kuma Iraq.
CPJ wacce ke tattara bayanan kisan da aka yi wa ma’aikan kafafen yada labarai tun daga shekarar 1992, ta ce daga shiga wannan shekarar ta 2025, an kashe ƴanjarida 6, lamarin da ya sanyata nuna fargaba kan girmar matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI