Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa ya zama wajibi a kubutar da Nahiyar Turai da ciwon kyamar Islama.
Shugaba Erdoğan, ya yi tsokaci akan karuwar nuna kyama ga addinin Islama a cikin 'yan kwanakin nan a Nahiyar Turai.
Shugaba Erdoğan ya yada a shafinsa ta twitter da cewa,
"Idan kasashen Turai na sonkare da kiyaye matsayinsu a tsarin siyasa da tattalin arzikin kasa da kasa, dole ne su hanzarta kawar da cutar kyamar Islama dake yaduwa a cikinsu. In ba haka ba, wacanan cutar za ta durkushe duk Turai daga Faransa zuwa Jamus."