Koriya ta Arewa ta bayyana sukar da shugaban Amurka Joe Biden ya yi a kan gwajin makami mai linzami a matsayin "tsokana da fyade akan mataki da hakkin kare kai"
Kanfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa ta (KCNA) ta rawaito cewa mataimakin shugaban majalisar kasar Ri Pyong Cho,ya yi kakkausar suka akan sukar da Biden ya yi wa gwajin makami mai linzamin kasarsa.
Da yake sukar cewa Amurka tana gwada makamai masu linzami a yankin Penisulan Koriya kuma tana tura manyan kaddarorinta na soja da ke kewaye da zirin Koriya, Ri ya bayyana cewa sukar da gwamnatin Washington ta yi game da gwaje-gwajen makaman kare dangi na Koriya ta Arewa wata dabara ce ta 'yan daba.
Ri ya jaddada cewa Amurka da Koriya ta Kudu na yi musu barazana ta fuskar soja kuma Koriya ta Arewa ba ta da wani zabi face ta gina wani karfi na zahiri don kare kanta, ya kara da cewa za su ci gaba da fadada karfin sojin kasar.
Shugaba Biden a ranar 25 ga watan Maris ya yi sharhi akan gwajin makami mai linzamin Koriya ta Arewa, inda yake cewa;
"Tare da wadannan gwaje-gwajen, Koriya ta Arewa ta karya kudurin Majalisar Dinkin Duniya na sakin layi 1718. Muna tuntuɓar abokan kawancenmu da kawayenmu a yankin. Idan suna son haɓaka tashin hankali, za mu ba da amsa da ta dace. Amma a lokaci guda, a shirye nake don diflomasiyya. Wannan diflomasiyyar ya kamata ta haifar da batun warware nukiliya ne kawai.