"Rashin janye sojojin Amurka daga Afghanistan zai gurbata shirin zaman lafiyar kasar"

"Rashin janye sojojin Amurka daga Afghanistan zai gurbata shirin zaman lafiyar kasar"

Wakilin shugaban kasar Rasha na musanman a Afghanistan Zamir Kabulov ya bayyanacewa jirkinta janye sojojinta da Amurka ke yi daga Afghanistan lamari ne da zai takurawa shirin samar da zaman lafiya a kasar. 

Kabulov dake jawabi ga kanfanin dillancin labaran Rasha ta Rus Ria, ya bayyana cewa da farko Amurka ta yi yunkurin janye sojojinta daga Afghanistan kafin 11 ga watan Satumba, amma hakan ya jinkirta bayan yarjejeniyar da Amurka ta yi da Taliban a Doha babban birnin Katar a ranar 29 ga watan Febrairu 2020.

Ya kara da cewa wanan zai tagaryara shirin samar da zaman lafiya a kasar sabili da yarjejeniyar Amurka da Taliban cin amana ne.

Da yake bayyana cewa Taliban ta kalubalanci matakan da Amurka ta dauka Kabulov ya kara da cewa ya kamata abokan aikinmu su tabbatar da hakan ga Kungiyar ta Taliban. 

 

 


News Source:   ()