Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa nuna wariyar launin fata a kasashen Turai musanman a Faransa ta rikide daga ta al'ada zuwa ga abinda hukumar kasar ke tallatawa.
Ya kara da cewa "A yau muna ganin yadda wariyar launin fata da nuna banbanci ke neman zama abinda hukumomin kasashen Turai ke kokarin runguma"
A jawabin da shugaba Erdogan ya yi bayan taron kolin majalisar ministocin Turkiyya ya jadadda cewa,
"'Yan siyasar Turai na kokarin boye rashin iya aikinsu ta hanyar nuna kyama ga baki da Musulmi"
A yau muna ganin yadda wariyar launi da nuna babbanci ke kara samun gurin zama a ma'aikatun kasashen Turai musanman a Faransa.