Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa bayan harin makamai masu guba akan farar hula a Siriya a shekarar 2017, ya yi niyyar bayar da umarni a kashe shugaban kasar Siriya Bashar Asad amma Ministan Tsaron wannan lokacin Jim Mattis bai goyi bayan hakan ba.
Trump, a shirin "Fox and Friends" da gidan talabijin din Fox ke gabatarwa ya bayar da amsa akan ikirarin da dan jarida Bob Woodward ya yi a cikin littafinsa da cewa Trump ya yi niyyar bayar da umarni a kashe Bashar Asad bayan harin makamai mai guba a shekarar 2017 a Siriya.
Trump, ya bayyana cewa na zabi a kashe Asad. Amma ministan tsaro na wannan lokacin Jim Mattis ya kalubalanci hakan, ya kara da cewa Mattis janaral ne mai kima da daraja sosai.
A yayinda aka tambayi Trump ko ya yi da-na-sanin rashin kashe Asad ya bayyana cewa,
A'a ban yi da-na-sani ba, zan iya daukar matakai domin rayuwarsa ko mutuwarsa. Da na so da na kashe shi amma Mattis ya kalubalanci hakan.