Ministan harkokin wajen Iran Muhammed Jewad Zarif ya bayyana cewa wakilan Isra'ila na shirin kaiwa sojojin Amurka dake Iraki hari da zummar Trump ya zargi Iran da kai harin ya kuma yake ta.
Zarif ya fitar da wannan sanarwar ne a shafinsa ta Twitter inda ya bayyana cewa,
"Dangane ga bayanan da muka samu a asirce, wakilan Isra'ila na shirin haifar da yaki tsakanin Iran da Amurka ta hanyar kaiwa sojojin Amurka dake Iraki hari lamarin da zai sanya Amurkan ta zargi Iran da kai harin ta kuma fara yaki da ita."
Zarif ya yi kira ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya bude idonsa domin kada ya fada a cikin tarko, domin ko wani irin harin da aka kaiwa Iran za ta mayar da martanin da ya dace.