"Iran ba ta kalubalanci kasancewar sojojin Turkiyya a Siriya da Iraki ba"

"Iran ba ta kalubalanci kasancewar sojojin Turkiyya a Siriya da Iraki ba"

Ministan harkokin wajen Iran Muhammed Jevad Zarif ya karyata ikirarin da ake yadawa wai "ya kalubalanci kasancewar sojojin Turkiyya a Siriya da Iraki"

An rinka yada jita-jitan cewa ma'aikatan harkokin wajen Iran ta bayyana cewa minista Jarif ya yi wasu bayanai dake kalubalantar wasu matakan Turkiyya.

Ma'aikatar ta bayyana cewa maganganun da aka danganta ga minista Jarif basu da kan gado kuma shaci fadi ne kawai.

"Waɗannan kalmomin ba su da tushe kuma ba su da mahimmanci da ya cancanci amsa." 

A wani sanarwa da aka fitar ta shafin sadar da zumuntar gidan talabijin din Al Arabiya ta kasar Saudiyya an bayyana cewa ministan harkokin wajen Iran Jarif ya kalubalanci kasancewar sojojin Turkiyya a Siriya da Iraki wanda kafar ta bayyana a matsayin kuskure.

 


News Source:   ()