Shugaban Majalisar Dattawan kasar Turkiyya Mustafa Şentop ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa dake zargin Turkiyya da rikita lamurkan kasashen Larabawa ta ci amanan tsarin Falasdin wanda ya kasance babban maslahar duniyar Islama.
Şentop ya yada a shafinsa ta Twitter inda ya kalubalanci kasar hadaddiyar Daular Labarawa (HDL),
"Kasar da ta kasance 'yan amshin shanta wacce bata da ra'ayin kanta dole ta kasance cikin damuwa da zullumin irin matakan da Turkiyya ke dauka na kare muradu da mutuncin Falasdin"