"Duniya za ta fuskanci annobar da ta fi Korona muni"

"Duniya za ta fuskanci annobar da ta fi Korona muni"

Shugaban kanfanin BioNTech wanda ya yi hadaka da kanfanin Pfizer wajen samar da allurar riga-kafin Korona Ferfesa Ugur Sahin ya bayyana cewa Covid-19 bai kasance mafi munin annobar da duniya za ta fuskanta ba.

Sahin da yake jawabi ga kafar yada labaran Bloomberg ya kafa hujja da cewa kwayar cutar Korona da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana a matsayar annoba a shekarar bara ta shirye duniya ne akan abubuwan da zasu faru nan gaba.

Ya kuma tabbatar da cewa annobar Korona ba za ta kasance mafi muni da duniya za ta fuskantaba, anan gaba za'a iya cin karo da annobar da ta fi Korona muni sabili da haka ya zama wajibi a shirya tarbon wannan yanayin.

Da yake bayyana cewa har ila yau duniya na kokarin cimma allurar riga-kafin Korona bayan fiye da shekara daya da bulluwar cutar, ya bayyana cewa hakan bai kamata ba.

Ga dukkan alamu Covid-19 ba zai kasance mafi munin annobar da za ta bulla a duniya ba, sabili da haka mafi a'ala shi ne ga gwamnatoci da kanfunan magani su shirya samar da allurar riga-kafi cikin watanni uku da bulluwar ko wace irin cuta.

 


News Source:   ()