"Ba zamu sulhunta da Isra'ila ba sai an kafa kasar Falasdin bisa taswirar 1967"

"Ba zamu sulhunta da Isra'ila ba sai an kafa kasar Falasdin bisa taswirar 1967"

Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Sheik Faysal Bin Ferhan ya bayyana cewa daidaitawa da Isra'ila lamari ne da zai kasance mai fa'ida ga tattalin arziki, tsaro da jin dadin al'umma a yankin baki daya.

Bin Ferhan a hirar da ya yi da CNN ya bayyana cewa bai da sanin ko kasarsa za ta shirya da Isra'ila a cikin 'yan shekarun ko kuwa a'a.

Bin Ferhan, ya bayyana cewa daidaitawa da Isra'ila lamari ne da zai fa'idantar da tattalin arzikin, tsaro da jin dadin al'umman yankin baki daya.

Bin Ferhan ya kara da cewa idan har ba a kawo karshen matsalar Falasdin ba, ba'a kuma kafa kasar Falsadin bisa ga taswirar shekarar 1967 ba shirin samar da daidaito da Isra'ila lamari mawuyaci.

Bin Ferhan ya kara da cewa kasar Saudiyya ta bayyana cewa idan aka kafa kasar Falasdin bisa taswirar shekarar 1967 da babban birninta a matsayar Gabashin Kudus za ta daidaita da Isra'ila.

 


News Source:   ()