"Azerbaijan ta baiwa Armeniya dama ta karshe na ta fice daga yankunan da take mamaya"
Kasar Turkiyya ta sanar da cewa kasar Azerbaijan ta baiwa Armeniya dama ta karshe da ta fice daga yankin Nagorno-Karabakh da take mamaya.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ce ta fitar da sanarwar cewa a yau Azerbaijan da Armeniya sun cimma matsaya akan yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sanarwar ta kara da cewa,
"A rikicin da ya barke tsakanin Azerbaijan da Armeniya a ranar 27 ga watan Satumba, Azerbaijan da nunawa duniya cewa tana da karfi da ikon da za ta karne dukkanin yankunata dake karkashin mamayar Armeniya na tsawon shekaru 30. A wannan yanayin kasa da kasa baki daya sun yi kira da a tsagaita wuta. Azerbaijan kuwa ta baiwa Armeniya dama ta karshe da ta fice daga dukkanin yankunan da take mamaya"
Kasar Azerbaijan ta baiwa Armeniya dama ta karshe na ta fice daga dukkanin yankunan da take mamaya a amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta domin samun damar kaiwa bil adama dauki da kuma yin musayar firsunoni da wadanda suka rigamu gidan gaskiya tsakjanin kasashen.
Sai dai hakan baya nufin kawo karshen rikicin baki daya. Turkiyya dai ta kasance tare da kasar Azerbaijan kuma za ta ci gaba da goya mata baya a koda yaushe.