"Armeniya ta sake nuna kanta a matsayar babbar makiyar zaman lafiyar yankin"

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa Armeniya ta sake nuna cewa ita ce babar makiyar dake kalubalantar zaman lafiya da sukunin yankin.

Shugaba Erdoğan, ya yi jawabi akan harin da Armeniya ta kaiwa Azerbaijan inda ya yada a twitter da cewa,

"Armeniya wacce ta kaiwa Azerbaijan hari, ta sake bayyana kanta a matsayar babar mai kalubalantar zaman lafiya da sukunin yankin. Al'umman Turkawa kamar yadda muka saba zamu ci gaba da kasancewa tare da Azerbaijan"

Shugaba Erdoğan, ya kara da cewa:

"Hukumomin kasa da kasa sun sake bayyana kansu a matsayin wadanda ke nuna wariya da fifiko, kasancewar yadda suka kasa mayar da wadataccen martani akan irin ta'asar harin da Armeniya ta kaiwa Azerbaijan. Kiminin shekaru 30 kenen da kasashen Minsk uku (Rasha, Amerika da Birtaniya ) suka kasa ko kusa da kaiwa ga hanyar kawo karshen matsalar kasashen. A yayinda muke kira ga al'umman kasar Armeniya su kalubalanci irin yadda gamnatin kasarsu ke daukar matakan tsokana da kuma amfani dasu a matsayar 'yan amshi shata, muke kuma kira ga duniya baki daya ta kalubalanci zalumci ta kuma goyi bayan Azerbaijan"

Muna kira ga kowa ya kasance tare da Azerbaijan a wannan mujadalar.

"A yau tattaunawar da na yi da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev mun sake nuna cewa muna tare da kasa da al'umman Azerbaijan, Turkiyya da Azerbaijan kasa biyu ne al'umma daya" Zamu ci gaba da karfafa 'yar uwarmu Azerbaijan.

 


News Source:   ()