Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa a cikin watanni uku an kashe farar hula 215 a rikicin da ake ci gaba da tafkawa a kasar Yaman.
Hukuma Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Yaman ta yada a twitter a rubuce da cewa a sanadiyar yakin da ake ci gaba da yi a kasar ta Yaman tsakanin watannin Yuli, Agusta da Satumba an kashe farar hula 215.
Sanarwar ta kara da cewa, iayali da dama sun kasance cikin halin neman agajin gaggawa.
AN dai dauki tsawon lokaci ana tafka rikici tsakanin mambobin kungiyar Houthi da halastacciyar gwamnation kasar ta Yaman.
Houthi sun kasance suna kula da ikon babban birnin kasar Sana da sauran yankunan nbirnin tun daga watan satumabr shekarar 2014 kawo yanzu. Kasr Saudiyya kuwa daga watan Maris din 2015 ta fara jagorantar kungiyar Houthi a kasar.