Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta bayyana cewar akwai bukatar dala biliyan 31.3 domin yin gwaji, magani da samar da allurar rigakafin kwayar cutar Covid-19 a cikin watanni 12 dake tafe.
A taron bidiyo konferans tare da babban sakataren WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda wakiliya na musanman na "ACT-Accelerator" Ngozi Okonjo-Iweala ta halarta ta bayyana cewar a kasashe marasa karfin tattalin arziki zai dauke su a kallan watanni 12 kafin su iya kammala gwaje-gwaje da kuma magance corona haka kuma samar da allurar riga-kafi ka iya daukar wasu watanni 18"
Tsohuwar mataimakiyar shugaban babban bankin duniya Okonjo-Iweala ta bayyana cewa akwai bukatar dala biliyan 31.3 domin yin gwaje-gwaje da daukar dawainiyyar warkarwa daga kwayar cutar corona da kuma samar da alllurar riga kafinta a cikin watanni 12.