Sojoji 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'Yan ta'addar Taliban suka kai kan cibiyar jami'an tsaro da ke kan iyaka a jihar Paktiya din Afganistan.
Ma'aikatar Tsaro ta Afganistan ta sanar da cewar 'yan ta'addar sun kai hari cibiyar soji ta gundumar Dand-i Patan da ke jihar Paktiya.
Sanarwar ta ce an kashe sojoji 14 tare da jikkata wasu 3 sakamakon harin.
An bayyana cewar sakamakon arangamar da ta biyo bayan 'yan Taliban ma sun tafka asara.
Har yanzu Taliban ba ta ce komai ba game da batun.