Wani yaro karami a gundumar Mare da ke arewacin Siriya ya mutu sakamakon fashewar bam din da 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK suka dasa.
An bayyana cewar wani daga cikin yara da suka fita waje wasa a gundumar ta Mare ne ya taka bam din.
Lamarin ya afku a kauyen Isnubbul da Mayakan Kasa na Siriya suke fafata rikici da 'yan ta'addar YPG/PKK suke yawan yin arangama, kuma yaron ya mutu.
A ranar Litinin din nan ma wani bam da aka binne a gundumar Bab ya fashe tare da jikkata yara kanana 2.