'Yan sandan Birtaniya ta bayyana harin da ka kai da wuka a matsayin ta'addanci
Hukumar 'yan sandan kasar Birtaniya ta bayyana harin da ka kai da wuka a wani gari dake kusa da Landan da ya yi sanadiyar rayukan mutane uku a matsayin harin ta'addanci.
A bayanin da ya fito daga hukumar 'yan sandan Thames Valley, hukumar 'yan sanda ta fitar da sanarwa a rubuce inda ta bayyana harin da aka kai a garin Reading mai nisan kilomita 60 daga Landan a matsayin harin ta'addanci.
A marecen shekaran jiya ne aka kai hari da wuka inda aka kashe mutum 3 da kuma raunana wasu uku. An kame wani dan shekara 25 wanda ake zargi daya daga cikin wadanda suka kai harin ne.
Kafafen yada labaran cikin gida sun bayyana cewa maharin dan gudun hijira ne da ya fito daga kasar Libiya.