Sanadiyar kawo karshen shirin samawa 'yan gudun hijira matsuguni da Tarayyar Turai ke yi a Girka 'yan gudun hijirar kasar zasu zasa gidajen zama.
An bayyana cewa kimanin 'yan gudun hijara dubu 10 dake zama a cikin giidaje da wasu sansanoni a babban birnin kasar Atina zasu rasa matsugunansu sanadiyar kawo karshen tallafin kudaden da ake basu a karshen wannan watan.
Kamar yadda aka dinga yadawa a shafukan sadar da zumunta dubun dubatan 'yan gudun hijira a kasar Girka sun taru a gaban ofishin Nahijar Turai na kasar domin kira ga hukumar da ta kara wa'adin tallafin gidajen da take basu.