An sanar da cewa kifewar jirgin roba dauke da 'yan gudun hijira a yankin garin Safaks dake kasar Tunisiya ya yi sanadiyar rayukan mutum 55.
Shugaban rundunar sojin yankin Murad al-Mishri ya bayyana cewa a tsibirin Kerkennah dake karkashin garin Safak jirgin roba na 'yan gudun hijira ya kife tare da hallaka mutum 55.
An bayyana cewar gawarwakin da aka gano sun hada da 28 na mata, 25 na maza da kuma biyu yara daga cikin yaran akwai mai shekaru 3 dayan kuma 2.
Daga cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiyr an bayyana cewar mafi yawansu 'yan kasar Ivory Coast ne inda daya dan kasar Tiunisiya sauran kuma ba'agane ko 'yan ina ne ba.