An sanar da kashe wani babban jami'in tsaron kasar Iraki mai suna Hisham al Hashim a wani hari da aka kai da bindiga a Bagdad babban birnin kasar.
Dangane ga bayanan da suka fito daga kafar yada labaran cikin gidan kasar da kuma shugaban harkokin watsa labarai Saad Maan, AL Hashim ya rasa ransa sanadiyar harin bindiga da aka kai yayinda yake a kofar gidansa.
An yi ikirarin cewa Hisham Al Hashim ya kasance wanda kungiyar Hizbullah dake samun goyon bayan Iran ke kalubalanta.