'Yan bindaga sun kashe mutum 24 a Mexico

'Yan bindaga sun kashe mutum 24 a Mexico

An sanar da cewa harin da 'yan bindiga dadi suka kai a wata cibiyar fadakarwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 24.

Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gidan Mexico suka rawaito, an kai hari da bindiga a wata cibiyar da ake nazartar da masu shan miyagun kwayoyi dake garin Irapuato  a jihar Guanajuato lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 24 da raunanna wasu 7/

Babban skataren tsaron Irapuato, Pedro Cortes Zavala ya sanar da cewa an kai wadanmda suka raunana a asibiti mafi kusa ya kara da cewa a cibiyar dake mutane 35 lamarin ya sanya wasunsu sun tsere.

Zavala da ya kara da cewa wadanda suka kai harin sun zone saman ababen hawa sai dai bai bayyana ko su wanene keda alhakin kai harin ba.


News Source:   www.trt.net.tr