'Yaranmu na mutuwa a hannunmu': Ambaliyar ruwa ta addabi Sudan ta Kudu

'Yaranmu na mutuwa a hannunmu': Ambaliyar ruwa ta addabi Sudan ta Kudu

An sanar da cewa ambaliyar ruwa ta sanya al’umma wasu yanki a Sudan ta Kudu na sha da wanka da ruwan da suka kwararo daga ban dakuna.

Kimanin mutum miliyan daya ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba samu a tarihin kasar. Hakan dai ya afku ne sanadiyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar.

Hakan ya haifar da lalata gonaki lamarin da ya sanya samun karancin abinci a kasar ta Sudan ta Kudu.

A ziyarar da kanfanin dillancin labaran Associated Press (AP) ta kai yankin tsohon garin Fangak ta rawaito cewa mata na tafiyar awanni a cikin ruwan da ya kai musu ga kirji domin samun abinci a yayinda cututtukan zazzabi, amai da gudawa ke addabar yankin.

Regina Nyakol Piny, mai yara tara daga kauyen Wangchot ta bayyana cewa a yanzu tana zama ne a wata makarantar firaimare bayan ambaliyar ruwan ta rusa gidajensu.


News Source:   ()