'Yan tawayen Taliban sun kashe 'yan sanda 5 a Afganistan

'Yan tawayen Taliban sun kashe 'yan sanda 5 a Afganistan

'Yan sanda 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawayen Taliban suka kai kan wata cibiyar jami'an tsaro da ke jihar Badgis din Afganistan.

Wakilin Majalisar Shura ta Badgis Muhammad Nasir Nazari ya bayyana cewa, 'yan tawayen sun kai hari kan caji ofis din 'yan sanda na gundumar Ab Kemeri da ke jihar Badgis.

Nazari ya shaida cewar, an kashe 'yan sanda 5, an kuma jikkata wasu 3 sakamakon harin.

Jami'in ya kara da cewar, bayan aikawa da jami'an tsaro zuwa yankin an fatattaki 'yan ta'addar.

A gefe guda, 'yan tawayen na Taliban sun sake kai hari kan caji ofis din 'yan sanda a jihar Gor tare da kashe jami'an tsaro 2.

 


News Source:   ()