Fararen hula 5 sun rasa rayukansu, wasu 85 sun jikkata sakamakon harin bam da mota da 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG suka kai a yankin Azez na arewacin Siriya.
An kai wadanda aka jikkata a kauyen Sijju na Azez da ke hannun 'yan adawa zuwa asibitocin yankin da kuma na Turkiyya.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewar 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG ne suka kai harin a yankin da aka kubutar daga hannunsu, kuma sun ki daukar nauyi ne saboda fararen hula sun mutu tare da jikkkata.
A safiyar Lahadin nan mutane 13 sun jikkata sakamakon fashewar bam din da aka dasa a cikin motar Mayakan Kasa na Siriya.
Daga yankin Tel Rifat da ya kamata 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG su bari karkashin yarjejeniyar Turkiyya da Rasha ta 22 ga Oktoba 2019,suna yawan kai hare-hare yankunan Bab, Azez, Jarabulus da Afrin.