'Yan ta'addar a ware na YPG/PKK da ke ci gaba da mamayar gundumar Tel Rifat ta arewacin Siriya sun kai hari da makamin roka zuwa Afrin inda fararen hula 2 a suka hada da yaro karami 1 suka mutu. Wasu fararen hula 10 kuma sun jikkata.
'Yan ta'addar na ci gaba da zama a yankin duk da cewar, yarjejeniyar da Turkiyya da Rasha suka kulla a ranar 22 ga Oktoban 2019 ta tanadi su fice daga cikinsa.
Sakamakon hari da makamin roka da 'yan ta'addar suka kai Afrin fararen hula 2 a suka hada da yaro karami 1 suka mutu. Wasu 10 kuma sun jikkata.
Wasu gidaje da ke yankin sun samu matsala sakamakon fadowar makamin rokar.