Daga yankin Tel Rifat na Siriya da 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK suka mamaya, an harba makami mai linzami zuwa yankin Meryemin da ke yammacin Afrin da aka kori 'yan ta'adda daga ciki a yayin Farmakan Reshen Zaitin.
An bayyana cewa, makami mai linzamin ya fada kan wata mota tare da jikkata fararen hula 3.
'Yan ta'addar YPG/PKK da aka kora daga Afrin a karkashin Farmakan Reshen Zaitin, na ci gaba da mamayar Tel Rifat.
A ranar 20 ga Janairun 2018 ne Dakarun Kasa na Siriya suka fara kai Farmakan Reshen Zaitin inda suka fatattaki 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK daga yankin Afrin a ranar 18 ga Maris.