Akalla mutum daya ya ji rauni sakamakon kungiyar ta'adda ta aware ta YPG/PKK da ta bude wuta kan wasu gungun matasa da ke gujewa dokar tilasta musu shiga kungiyar a yankunan da ta mamaye a arewa maso gabashin Siriya.
A lardunan Deir ez-Zur da Hasakah, inda larabawa ke da yawa, YPG/PKK na tilasta wa mutane shiga kungiyar.
YPG/PKK ta kame matasa kusan 15 a tsakiyar gundumar Qamishli na Hasakah don tilasta musu shiga kungiyar.
An samu labarin cewa wasu daga cikin matasan da ke adawa da shiga kungiyar sun yi kokarin tserewa kuma a kalla matashi daya ya samu rauni sakamakon harbin da aka yi musu.
'Yan ta'addan, wadanda suka taba aiwatar da irin wannan aikin a da, sun kame daruruwan maza 'yan shekaru 18 zuwa sama a cikin 'yan watannin a tsakiyar garin Hasakah da kuma a gundumar Qamishli, a samamen da suka kai kan gidaje da wuraren bincike.
'Yan ta'addar na kai samari da aka kame zuwa wuraren horarwa a Hasakah, a arewa maso gabashin kasar.