Masu tsaron kauye 3 da soja 1 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'Yan tawayen Taliban suka kai wa wata cibiyar tsaro da ke gundumar Hoja Bahaddin din jihar Tahar a Afganistan.
Kakakin Helkwatar 'Yan sandan jihar Tahar, Halil Esir ya sanar da cewar 'yan tawayen na Taliban sun kai hari da bindigu a cibiyar tsaro ta kauyen Lala Guzer da ke gundumar Hoja Bahaddin.
Ya bayyana cewar an kashe masu tsaron kauye 13 da soja 1, inda aka jikkata wasu jami'an tsaro 4 sakamakon harin.
Esir ya kara da cewar a arangamar da ta biyo bayan kai harin, an kashe 'yan tawayen Taliban da dama.
Har yanzu Taliban ba ta ce komai ba game da lamarin.