'Yan ta'addar a ware na PKK da mayakan Peshmerga sun fafata rikici a garin Duhok Iraki.
Majiyoyin yankin sun tattauna da kamfanin dillancin labarai na Anadolu inda suka ce, wasu 'yan ta'addar PKK ne suka yi yunkurin wucewa ta shingen binciken ababan hawa na mayakan Peshemrga da ke kauyen Dereshin na gundumar Amedi a garin Duhok wanda sakamakon haka arangama ta barke.
Majiyoyin sun ce, mayakan Peshmerge sun bude wuta kan motar 'yan ta'adda tare da jikkata 3 daga cikinsu bayan da suka ki tsayawa a wajen.
A gefe guda kuma, an samu wata arangamar daban a garin Duhok inda aka kashe sojan Peshemrga 1.