Jami'an tsaro 4 da suka hada da dan sanda 1 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Dash suka kai a garin Kerkuk na kasar Iraki.
Manjo Janar Yahya Rasul Abdullah na Rundunar Sojin Musamman ta Ma'aikatar Tsaron Iraki ya fadi cewa an kai wa Daesh hare-hare ta bangarori 3 a yankin Gayda.
Abdullah ya ce an kashe 'yan ta'addar Daesh 3 a harin, kuma sakamakon fashewar wani bam da 'yan ta'addar suka binne a gefen hanyajami'an tsaro 4 da suka hada da dan sanda 1 sun mutu.
Manjo Janar din ya kara da cewar an fara kai hare-hare na musamman kan Daesh a unguwar Mekishife ta jihar Salahaddin da kuma yammacin tafkin Dijle.