'Yan ta'adda sun kashe sojoji biyu a Siriya

'Yan ta'adda sun kashe sojoji biyu a Siriya

An sanar da cewa harin ta'addanci da aka kai da mota makare da bama-bamai a sansanin sojan Siriya mai adawa da gwamtain kasar a garin Ras al-Ayn sojoji biyu sun rasa rayukansu inda wasu biyu kuma suka raunana.

An kai harin ne a inda sojojin ke gudanar da bincike a kauyen Tel Jeneb dake karkashin garin Mebruke a yankin Ras al-ayn da mota dankare da bama-bamai.

A binciken da ka fara ana hasashen cewa kungiyar ta'addar YPG/PKK ce keda alhakin kai harin.

A ranar 12 ga watan Oktoban 2019 ne dakarun Turkiyya suka kakkabe yankin Ras-al ayn daga 'yan ta'adda.

Kungiyar ta'addar YPG/PKK daga yankunan. Ayn Isa da Tel Temir suna kaiwa farar hulan dake yankunan Ras al ayn da Tel Abyad hari akai akai.

 


News Source:   ()