Harin ta'addancin da aka kai kasar Nijer ya yi sanadiyar rayukan farar hula 56.
Kamar yaffa kafafen yada labaran cikin gidan kasar Nijer suka sanar a kauyukan Tchombangou da Zaroumdareye dake kan iyaka da kasar Mali 'yan ta'adda suka kai hari da bindiga.
A harin mutum 56 suka rasa rayukansu inda kuma 20 suka raunana.
Ministan harkokin cikin gidan Nijer Alkache Alhada ya tabbatar da harin inda ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro a yankin.