'Yan ta'adda sun hallaka mutum 18 a iyakar Nijar da Mali

'Yan ta'adda sun hallaka mutum 18 a iyakar Nijar da Mali

Fararen hula 18 ne suka mutu sakamakon harin ta'addancin da aka kai kan iyakar Nijar da Mali.

A cewar sanarwar da aka yada a shafin sada zumunta na kungiyar mai zaman kanta ta "Urgence Tillbaeri", wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a yankin Banibangou da ke yammacin kasar Nijar.

Mutane 18 ne suka mutu yayin da 4 suka jikkata a lamarin. Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Haka kuma a ranar 25 ga watan Yuli ma an kai wani hari a yankin da ya yi sanadiyar rayuka 14.

Burkina Faso, Mali da Nijar, wadanda aka fi sani da "iyakar kasashe 3" a yankin Sahel, sun fuskanci hare-hare daga DAESH da kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Al-Qaeda a shekarun baya bayan nan.


News Source:   ()