'Yan sandan Isra'ila sun kashe wani matashin Bafalasdine bisa ikirarin cewar ya yi yunkurn kai hari da wuka a Gabashin Kudus da Yahudawa suka mamaye.
Sanarwar da Kungiyar Red Crescent ta Falasdin ta fitar ta ce 'yan sandan Isra'ila sun yi amfani da harsashin gaske wajen harbin Bafalasdinen a yankin Tsohon Garin Kudus da Masallacin Aksa yake.
Sanarwar ta ce 'yan sandan na Isra'ila sun hana jami'an Kungiyar ta Red Crescent ta kula da lafiyar matashin da aka jikkata.
A gefe guda, 'yan sandan Isra'ila sun fitar da sanarwar cewa an harbe Bafalasdinen ne sakamakon yunkurin kai hari da wuka da ya yi a yankin.
Jaridun yankin sun ce dan sandan Isra'ila ya samu rauni inda Bafalasdinen kuma ya mutu.
Bayan lamarin, Isra'İla ta rufe dukkan kofofin shiga Masallacin Aksa.