'Yan sandan Isra'ila sun kai hari dab bama-bamai masu kara kan Falasdinawa bayan Sallar Juma'a a Masallacin Aksa tare da jikkata mutane 20.
Dubunnan Falasdinawa ne suka taru bayan Sallar Juma'a tare da yin Kabbara suna murnar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila.
Daga baya Falasdinawan sun so yin tattaki daga Masallacin Aksa zuwa tsohon garin Kudus.
Jami'an tsaron Isra'ila sun yi amfani da bama-bamai masu kara don tarwatsa su.
An jikkata Falasdinawa 20 sakamakon zaluncin na 'yan sandan Isra'ila.