'Yan sandan Isra'ila sun kaiwa Falasdinawa hare-hare

'Yan sandan Isra'ila sun kaiwa Falasdinawa hare-hare

'Yan sandan Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawa mazauna unguwar Shaikh Jarrah da ake barazanar korar su daga gidajensu da kuma wadanda suka zo taimaka musu.

Bayanan da aka samu daga shaidun gani da ido sun bayyana cewa, 'yan sandan Isra'ila sun zuba bola tare da rufe hanyar shiga dandalin unguwar Shaikh Jarrah, sannan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa 'yan jaridu da jama'ar da suka taro don goyon bayan mazauna Shaikh Jarrah.

Haka zalika 'yan sandan na Isra'ila sun karya kofar wani gida a unguwar Shaikh Jarrah tare da kai hari kan mazaunansa.

'Yan kama guri zauna na Isra'ila a ranar Asabar din da ta gabata sun harba hayaki mai sa hawaye kan mazauna unguwar SHaikh Jarrah da ke Gabashin Kudus da kuma Falasdinawan da suka taru don goya musu baya.

Tun daga ranar 13 ga Afrilu da aka fara Azumin Ramadhan zuwa yau ake ta samu rikici da dauki ba dadi a unguwar Shaikh Jarrah da ke Gabashin Kudusda kuma kewayen Masallacin Al-Aksa.


News Source:   ()