'Yan sandan Faransa sun kai sumame kan kungiya mai zaman kanta ta Musulmi mai suna Baraka City.
A babban birnin kasar Faransa, Paris matsin lamba ga kungiyoyi masu zaman kansu na Musulmai ya karu a makonnin da suka gabata.
'Yan sandan Faransa sun kai samame kan wata kungiya mai zaman kanta, Baraka City.
Sanarwar da aka fitar daga shafukan sada zumunta na Baraka City ta bayyana cewar gidan wanda ya kafa ta Idriss Sihamedi shi ma an kai masa samame.
An tsare Sihamedi a gaban yaransa.
An bayyana cewar 'yan sanda sun makala zoben karfe a hannun matar Sihamedi kuma suka nemi yaransu da su daga hannayensu.
Jami'an Faransa ba su yi wani bayani ba game da batun.
Ministan Cikin Gida na Faransa, Gerard Darmanin ya zargi Idriss Sihamedi da tallafawa ta'addanci.
A baya an wanke Baraka City daga tuhume-tuhumen zargin ta'addanci.