'Yan sandan Amurka sun sake harbe wani bakar fata

'Yan sandan Amurka sun sake harbe wani bakar fata

A garin Los Angeles na Amurka, 'yan sanda sun harbe wani bakar fata bisa dalilin sun tsayar da shi a kan kekensa ya ki tsayawa.

'Yan sandan sun yi ikirarin cewar mutumin da suka harbe har lahira ya tuka keke ba bisa ka'ida ba.

Labaran da jaridar Los Angeles Times ta fitar ta rawaito jami'in 'yan sandan yankin Brandon Dean na cewa, wasu jami'ansu biyu sun yi kokarin tsayar da wani bakar fata da ke tuka keke.

Dean ya ce mutumin bakar fata dan asalin Afirka ya ajje keken tare da fara gudu, kuma a lokacin da 'yan sandan suka isa inda yake sai ya kutufi daya daga cikinsu.

Ya kara da cewar a lokacin da ake kokawa da shi ne sai bindiga ta fado daga jikinsa wanda hakan ya sanya 'yan sandan suka bude wuta.

An bayyana cewar sakamakon bude wutar, bakar fata Dijon Kizzee mai shekaru 29 ya rasa ransa.

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga tare da yin tattaki zuwa ofishin 'yan sandan a ranar Litinin da lamarin ya afku.

Masu zanga-zangar sun dinga fadin cewar babu wani dalili da za a gabatar na ya dace a kashe bakar fatar, sun kuma dinga cewa "Babu Adalaci", "Babu Zaman Lafiya".


News Source:   ()