'Yan sanda sun sake kashe wani bakar fata a Amurka

'Yan sanda sun sake kashe wani bakar fata a Amurka

An sanar da cewa 'yan sandan jihar Louisiana dake Amurka sun harbe wani bakar fata mai suna Trayford Pellerin har lahira.

An yada faifan bidiyon afkuwar lamarin da ya faru a daren juma'a a Lafayette, Tarayyar 'Yancin Farar Hula (ACLU) ta yi kira da a gudanar da bincike akan lamarin.

Riundunar 'yan sandan jihar Louisiana, ta sanar da cewa jami'anta sun harbe wani mai suna Trayford Pellerin sabili da tayar da rigima da yayi da wuka a wata kasuwa.

Mutumin mai shekaru 31 an harbe shi ne yayinda yake kokarin shiga wani shago da wuka a hannunsa.

Kashe Pellerin ya haifar da giudanar da zanga-zanga abinda ya sanya 'yan sanada amfani da bam mai kara domin tarwatsa masu tarzomar.

Mahaifiyar mammacin Michelle Pellerin ta bayyana cewar danta nada matsalar rayuwa wanda ma anka baiwa taimako da dama a lokacin bikin sabon shekara. Ta kara da cewa sabili da matsalarsa ba mamaki 'yan sanda su dauka ko zai zama kalubale da hatsari ga al'umma ne.

Lawyan Michelle Pellerin ya bayyana cewa zasu shigar da kara akan kashe  Trayford Pellerin.

 


News Source:   ()