'Yan sama jannati sun tafi sararin samaniya don aiki a tashar ISS

'Yan sama jannati sun tafi sararin samaniya don aiki a tashar ISS

'Yan sama jannati sun tafi sararin samaniya don kafa sabbin na’urori masu amfani da hasken rana a Tashar Sararin Samaniya ta Duniya (ISS).

Dan sama jannati daga Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA), Shane Kimbrough da dan sama jannati daga Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Turai, Thomas Pesquet ne suka fara tafiyar zuwa sararin samaniya don ci gaba da kafa na’urorin masu amfani da hasken rana, wanda aka jinkirta saboda matsalolin fasaha a ranar Laraba.

Ana sa ran tafiyar ta su zuwa sararin samaniya zata dauki awanni 6.5.

Sabbin na’urorin zasu taimaka wajen biyan bukatun tashar ta sararin samaniya.

 

 

 


News Source:   ()