'Yan majalisun Birtaniya sun yi kira da a daina sayar wa Isra'ila da makamai

'Yan majalisun Birtaniya sun yi kira da a daina sayar wa Isra'ila da makamai

Wasu ‘yan majalisun Birtaniya sun nemi gwamnatin kasarsu da ta sanya takunkumi kan Isra’ila tare da dakatar da sayar mata da makamai akan karya dokar kasa da kasa kan hare-haren da take kaiwa Falasdinawa.

Ministan da ke da alhakin Gabas ta Tsakiya, James Cleverly, ya amsa tambayoyin 'yan majalisun a cikin shirin mai taken "Israel Gaza- Tsagaita Wuta Cikin Gaggawa" da aka gudanar a zauren majalisar.

Dan majalisar Jam'iyyar Labour Richard Burgon, wanda ya jagoranci zaman ya yi kira ga gwamnatin Birtaniya inda ya ke cewa,

"Shin ya kamata a kashe yaran Falasdinawa nawa ne, gidajen Falasdinawa nawa ya kamata a rusa, makarantu da gidajen Falasdinawa nawa ne ya kamata a jefawa bam gabanin a dauki matakin tilastawa Isra'ila ta dakatar da yakin da take yi da Falasdinawa?" 

Ya kara da cewa lokaci ya yi da za'a bayyana kasar Falasdinawa, domin su ma suna da 'yancin kafa kasa da kuma zama a cikinsa.

Burgon ya kuma yi kira ga gwamnati da ta daina sayar da makamai tare da sanyawa Isra’ila takunkumi, wacce ta karya dokokin kasa da kasa a hare-haren da take kaiwa Falasdinu.

Tsohon shugaban jam'iyyar Labour Party, Jeremy Corbyn, ya jaddada cewa jama'a na da 'yancin sanin alakar soja tsakanin gwamnatin Birtaniya da Isra'ila; ya kuma nemi Cleverly da ya yi bayanai kan hadin gwiwar soja tsakanin kasashen biyu.

Corbyn ya kuma tambaya ko an yi amfani da duk wani makami ko albarushin da Birtaniya ta sayar wa Isra'ila wajen jefa bam a Gaza.

Don kaucewa amsa wacanan tambayar, Cleverly ya bayyana cewa kasarsa tana da kakkarfan tsarin lasisin fitar da makamai kuma duk ana sayar da makaman yadda ya kamata.

Falasdinawa 227 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra’ila ta kai wa Gaza da take mamaya tun daga ranar 10 ga watan Mayu.


News Source:   ()