Wani sojan Peshmerga ya rasa ransa yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a garin Sulaymaniyah da ke Iraki.
Jami’in Jam’iyyar Dimokradiyya ta Kurdistan (KDP), Besam Ali ya bayyana wa manema labarai na cikin gida cewa wani sojan Peshmerga ya rasa ransa a harin da masu zanga-zangar suka kai wa ginin KDP da ke gundumar Pencivin na Sulaymaniyah.
Ali wanda ya sanar da cewa sojojin Peshmerga 2 sun ji raunuka a harin da yake magana, ya lura da cewa an kone wani ginin KDP a gundumar Hanekin na garin Diyala.
Bekir Abdullah, wani jami’in KDP a Pencivin, ya bayyana wa kafofin yada labarai na cikin gida cewa maharan ‘yan kungiyar ta’addar a ware na PKK ne.
Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyun da suka gabata ya karu zuwa 9 a zanga-zangar adawa da Gwamnatin Kurdawa ta Iraki (KRG) saboda jinkirin da aka samu na albashin ma'aikatan gwamnati a Sulaimaniyah da Halabja. Fiye da mutane 100 sun ji raunuka a lamarin.