An sanar da mutuwar yan gudun hijira 21 yan kasar Afirka sanadiyar kifewar kwale kwalen da suke ciki a yankin Tunisiya.
Wani jami'in gwamnatin Tunisiya ya bayyana cewa wani kwale kwale ya kife dauke da yan gudun hijira a yayinda yake kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.
Sanarwar ta kara da cewa yan gudun hijira 21 sun rasa rayukansu sanadiyar kifewar kwale kwalen.
Kawo yanzu ana ci gaba da binciken sauran mutanen da ba a gani ba.