'Yan fashin teku sun sace ma'aikatan jirgin ruwan Turkiyya 15 a Najeriya

'Yan fashin teku sun sace ma'aikatan jirgin ruwan Turkiyya 15 a Najeriya

An sanar da kaiwa jirgin ruwan Turkiyya hari a gabar tekun Najeriya inda aka kashe daya daga cikin ma'aikatan jirgin ruwan dan kasar Azabaijan.

An sanar da cewa, an kai hari kan wani jirgin ruwan Turkiya mai suna Mozart, mallakar wani kamfani da ke Istanbul, a mashigin tekun Guinea mil 100 daga Sao Tome.

A bayanin kamfanin daya daga cikin ma’aikata 19 da ke cikin jirgin da ya tashi daga Lagos, Najeriya zuwa Cape Town, Afirka ta Kudu an kashe shi, an sace 15, sannan 3 sun kasance a cikin jirgin tare da ‘yan fashin tekun.
Tuni dai an fara aikin ceto ma'aikatan da aka sacen.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sami bayanan abin da ya faru da kuma halin da jirgin yake ciki ta hanyar zantawa da Furkan Yaren, Kyaftin na 4 na jirgin ta wayar tarho.

Ya samu bayanin cewa jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa Gabon tare da ma’aikatansa 3 da suka tsira daga harin, haka kuma Erdoyan ya bayyana cewa yana bin lamarin sau da kafa kuma ya umurci dukkan jami'ai game da ceto ma'aikatan jirgin ruwan da aka sace.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya  Mevlut Cavusoglu ya zanta da Osman Levent Karsan, ma'aikacin kamfanin da jirgin, kuma ya isar da ta'aziyyarsa, yana mai jaddada cewa za a dauki matakan da suka dace don kubutar da ma'aikatan da aka sace da wuri-wuri kuma a mayar da su gidajensu lafiya.

Cavusoglu ya kuma kira Ministan Harkokin Wajen Azabaijan Ceyhun Bayramov inda ya jajanta akan wanda aka kashen, ya kuma yi alkawarin cewa  lokacin da jirgin ya sauka, za a fara aikin mika gawar zuwa Azabaijan ba tare da bata lokaci ba.

Turkiyya da na Najeriya da ma jakadojin kasashen dake kewaye da ita a Abuja sun fara aiki tukuru domin ceto wadanda aka sacen.

 


News Source:   ()