A babban birnin Afganistan, Kabul an kaiwa wata motar sojoji hari da bindiga lamarin da ya yi sanadiyar rayukan sojoji biyu.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tarik Aryen ya bayyana cewa a yankin Kote-i Sangi dake karkashin Kabul wasu wadanda ba'a san ko su wanenen ba sun kaiwa sojoji hari suna cikin mota.
Aryen, ya bayyana cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu inda maharan suka arce cikin daji.
Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin akan kowa ba.