An kashe mutane 88 a harin bindiga da aka kai a wasu yankuna dake jihar Kebbi dake arewacin kasar Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Nafi'u Abubakar ya bayyana cewa wasu da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a wasu yankuna dake jihar Kebbi.
Abubakar, ya kara da cewa harin ya yi sanadiyar rayukan mutum 88.
Nafi'u Abubakar, ya kara da cewa yayin da 'yan sandan jihar suka kewaye yankin an soma bincike akan lamarin.
Sanadiyar hare-haren da 'yan bindiga suka kai jihar a watan Afirilu 'yan sanda 8 sun rasa rayukansu.